saurare  da kallon  duniya

Bayanin kai aƙidar kariya

A matsayin ayyukansa da kuma dacewa da dokokin Faransa da Turai, musamman Dokokin Kariyar Bayani ta EU, France Médias Monde a shirye suke domin tabbatar da kariya, sirri da tsare bayanan kai na masu amfaninsu, abokan cinikansu, masu ra’ayi da masu samar da kaya, da kuma mutunta sirrinsu.

Aƙidar Kare Bayanan Kai na aiki a kan tattara bayanai da sarrafawa da ake yi a kan sassan yanar-gizon France Médias Monde (wato “Sassan yanar-gizon”), manhajojin kan layi na smartphone, tablet da wasu na’urorin hannu (wato “manhajoji”), da kuma yin amfani da sabis-sabis ɗinmu ko ƙunshin kan layi.

Sassan yanar-gizonmu da Manhajojinmu ba na yara ba ne sai dai in wakilansu bisa doka sun ba su dama.

Ana iya canje-canjen Aƙidar Kariyar Bayanan Kai. An fayyace cewa ƙila France Médias Monde ba za su gyara Aƙidar Kariyar Bayanan Kai ba a kowane lokaci, tare da ta’allaƙa ta da dokar yanzu. Ana sanar da Masu amfani game da waɗannan sauye-sauye cikin sauƙi ta hanyar abin da suka wallafa a kan layi. Muna ba da shawara cewa ka/ki dinga bincika sabuwar sigar da ke akwai.

Aƙidar Kariyar Bayanan Kai na saita tsaruka da hanyoyin sarrafa bayanai.

Tsarukan bayanai da kariyar sirri

1. Tara bayanan kai na abokan ciniki, masu ra’ayi da masu-amfani cikin adalci

An tara bayanan a cikin adalci da bayyanawa. An haramta ma France Médias Monde tara bayanan kai ba tare da sanar da mutumin da abin ya shafa ba, tare da abin da za a yi da bayanansu.

France Médias Monde na tara wannan bayani ne domin:

  • Samar da sabis-sabis ɗin da abokin ciniki ke buƙata,
  • cim ma buƙatar kulawar masu amfaninsu, abokan cinikinsu da masu ra’ayinsu.

France Médias Monde na sanar da masu amfani game da: saka kukis da wasu masu bin-sawu a sassan yanar-gizon da suke ƙirƙira; dalilansu; dokar da ke tare; da kuma zaɓin ƙin amincewa da su.

Domin Ƙarin Bayani Danna nan Kukis

2. Amfanin bayanan kai na abokan cinikinsu, masu ra’ayinsu da masu amfani

France Médias Monde na amfani da bayanan mutane domin tantancewa, samar da sabis-sabis da aka saya da shawarta abubuwa domin sha’awar abokan ciniki, masu ra’ayi da masu ziyara. Har wa yau, France Médias Monde na iya gudanar da nazarin rarrabewa dangane da bayanan.

France Médias Monde na bin tsarin dokokin da ke gudana dangane da kariayar bayanan kai da kuma hurumin kariya da rufin asiri. France Médias Monde na sanar da masu samar da sabis ɗinsu ne kawai game da bayanan kai da kuma tabbatar da cewa sun cim ma hurumin rufin asiri, amfani da kuma kariyar wannan bayani.

An haramta ma France Médias Monde sanar da bayanan kai ga abokan kasuwanci ba tare da sanar da abokin kasuwancinsu ba, masu ra’ayi, da masu ziyara, kuma ba tare da samar masu da damar ikon ƙin amincewa ba.

3. Mataikai da suka dace domin tabbatar da kariya bayanan kai na abokan cinikinsu, masu ra’ayinsu da masu amfani

France Médias Monde na tabbatar da kariyar bayanan kai da a ka mallaka masu, tun daga tushe zuwa rayuwar sabis-sabis ɗin sashen ko manhajoji.

  • Suna gudanar da matakan kariya da suka dace da muhimmancin bayanin domin kare bayanan kai daga shammacin maƙiyi, ko ɓata, sauyi ko fallasa ga wani da bai dace ba.
  • Naurar bayanan, saba da hanyoyin sadarwar da ake amfani da su domin sarrafa da adana bayanan kai na da na’urar kariya (ɓoye bayanai, fayawal, kasala, tsimi, da sauran su).
  • Ta ba da garantin kariyar musayar bayanai a halin cinikayya ko biyan kuɗi.
  • Tana amfani da damar isa ga ne kawai na na’ura bayanai ga waɗanda ke buƙatar su domin yin aiki.
  • Na ilimantar da ma’aikatansu a game da kariyar bayanan kai da aka samar masu a matsayin aikinsu da kuma tabbatar da cewa suna bin dokoki da ƙa’dojin wurin aiki.
  • Yana buƙatar masu samar da kayayyaki da su bi waɗannan tsare-tsaren kariyar.

Kariyar bayanai a France Médias Monde

1. Wane bayani ake karɓa kuma ta yaya?

Ta shiga Sassan yanar-gizonmu ko amfani da Manhajojinmu da sabis-sabis, France Médias Monde, masu samar da sabis ko abokan kasuwanci na iya karɓar bayanai tare da izininka.

Kai/ke ne ke samar mana da wasu bayanan, kamar sunayenka na farko da na ƙarshe, adireshin imel, lambar waya, ƙorafi ko wani ra’ayi da ka raba da mu.

Ana samar da wannan bayani ne yayin da:

  • ka/kin ƙirƙiri wani asusu a The France 24 Observers (EN, FR, AR, FA, ES) da/ko Le français facile avec RFI,
  • ka/kin shiga wani wasa ko wata gasa,
  • ka/kin tuntuɓe mu da kuma cika wani fam,
  • ka/kin rubuta wani jawabi,
  • ka/kin saya daya daga cikin wasiƙun labarunmu
  • ka/kin zazzage da amfani da manhajojinmu.

Ana iya karɓar wasu bayanai ta kai tsaye tare da izininmu, saboda aikinka a kan Sassan yanar-gizon da manhajoji daga kukis ko fasaha mai kamar haka kamar adireshin IP, bayanan haɗi da shiga yanar-gizo, abubuwan da ka fi so da sha’awa, da yankin da ake zaune.

Ana amincewa da wannan bayanin duk sanda ka/kin shiga Sassan yanar-gizonmu da Manhajoji.

2. Mene ne dalilan bayanan da aka karɓa?

Muna amfani da bayanan da aka karɓa domin:

  • Samar da ƙunshi da sabis-sabi waɗanda:
    • ke gane ka idan ka dawo cikin Sassan yanar-gizonmu ko amfani da Manhajojinmu;
    • kula da asusun Mai amfani da sanar da ku game da sababbin abubuwa game da asusunku da sabis-sabis ɗin da kuke amfani da;
    • amsa buƙatarka da aka gabatar a Sassan yanar-gizonmu da Manhajoji, da aka haɗa a kan fama-famai;
    • samar maka da Sabis-sabis da ƙunshin da ka tsara dangane da yankin da ka/ki ke zaune (ƙasa);
    • ba ka damar rubuta jawabai game da ƙunshin Sassan yanar-gizonmu da Manhajoji;
    • saita bayyanar ƙunshi da Sabis-sabis;
    • aika maka wasiƙun labarun da ingiza sanarwar, ƙararrawar labaru;
  • Tallata ƙunshinmu da sabis-sabis, da na abokan ma’amalarmu, waɗanda ke:
    • samar da ƙunshi domin sha’awarku da gudanar da tallar da ake hari;
    • aika sadarwa da auna muhimmancinsu;
  • Gudanar da nazari da rabe-rabe a kan ƙunshinmu da sabis-sabis domin:
    • kyakkyawar fahimatar masu amfani da Sassan yanar-gizonmu da Manhajojin;
    • gudanar da rabe bayanai da nazarin ƙididdiga domin bunƙasa da haɓaka Sassan yanar-gizonmu ko Manhajoji;
  • Domin tabbatar da kariyar bayananka.

    3. Su wane ne masu karɓar bayanan da aka karɓa?

    Bayanan da aka karɓa daga Sassan da Manhajoji na France Médias Monde ne.

    Masu samar da sabis ɗin France Médias Monde na iya tura ko duba su da sunan sarrafawa, rabe bayanai da sabis-sabis ɗin kwamfuta.

    France Médias Monde na buƙatar masu samar da sabis ɗinsu da su yi amfani da bayanin kai kawai domin gudanar da sabis ɗin da aka ba su, dangane da dokokin da suke aiki domin kariyar bayanan kai da rufin asirin wannan bayani.

    France Médias Monde na sanar da kai cewa sun cim ma yarjejeniya da abokin kasuwancin da zai iya ƙarɓar bayani game da kai. France Médias Monde ba su da abin gani game da wannan bayani. Muna gayyatar ka da ka tuntuɓi jerin ainihin abokan ma’amalarmu a aƙidar kukis: Kukis.

    4. A ina ake adana bayanin kai naka?

    Ana adana bayanin kai naka ne a Tarayyar Turai, ko a matattarar bayananmu ko na masu samar da sabis ɗinmu.

    A wasu lokuta, kuma musamman domin dalilan fasaha, ana iya adana bayani a sabar ba ta cikin Tarayyar Turai.

    5. Bayanin da aka tura wajen Tarayyar Turai

    Musamman saboda alaƙar ƙasa da ƙasa ta France Médias Monde, wasu daga cikin abokan ma’amalarmu suna zaune ne a wajen Tarayyar Turai Za a iya tura bayanin da aka karɓa zuwa ƙasashen da ba su a cikin Tarayyar Turai waɗanda suke da dokar kariyar bayanin kai ta daban da waɗanda ke cikin Tarayyar Turai

    A wannan hali, France Médias Monde na gudanar da hanyoyi domin tabbatr da kariyar da rufin asirin wannan bayani da kuma tabbatar da cewa tura bayani ya dace da tsarin doka: turawa zuwa wata ƙasa tare da tabbatar da isasshiyar kariya, saka hannun yarjejeniya da Hukumar Turai ta samar, ko wasu hanyoyin doka ko yarjejeniya domin tabbatar isasshiyar kariya.

    France Médias Monde na matuƙar buƙatar abokan ma’amalarsu da yin amfani da bayanan kai naka domin kula da ko samar da sabis-sabis ɗin da ake buƙata, da kuma kira ga abokan ma’amalarsu da su dinga aiki da bin dokoki domin kariyar bayanan kai da kuma mayar da hankali ga rufin asirin wannan bayani.

    Za a iya tura bayani zuwa wajen Tarayyar Turai, takamaimai, kasancewa daga cikin ayyukanmu kamar sabis-sabis ɗin kwamfuta a na’urorin France Médias Monde.

    6. Ta yaya kuma mene ne tsawon lokacin da ake adana bayaninka?

    France Médias Monde na ƙaddamar da duk matakan kulawa, fasaha da bayyana domin kare bayanin kai.

    Ana adana bayanin kai ne na tsawon lokacin da ake buƙata domin sarrafawa sai dai idan ana buƙatar cigaba da adanawa na wani tsawon lokaci bisa doka, ko sauraron ƙara

    Misalai:

    Dalil(i/ai) Bayani Tsawon lokacin adana
    Bayanin kasuwanci Sunan farko da na ƙarshe, kamfani, adireshin imel, saƙo Watanni 12 daga sauyi na ƙarshe
    Domin rohoton wata matsala, yin jawabi ko bayar da shawara game da Sashen yanar-gizon Sunan farko da na ƙarshe, adireshin imel, suna da sigar burauzar da a ka yi amfani da ita, saƙo Watanni 12 daga sauyi na ƙarshe
    Domin tuntuɓar wani ɗan jarida ko mai gabatarwa daga France Médias Monde Sunan farko da na ƙarshe, adireshin imel, saƙo Watanni 12 daga sauyi na ƙarshe

    7. Mene ne damarka?

    France Médias Monde sun dage da mutunta duk damar abokan kasuwancinsu, masu ra’ayinsu, da masu ziyartarsu tare da isa ga, gyara, ƙarin bayani da banbancin ra’ayi. An taƙaita na wanda abun ya shafa, yawo da damar sharewa daga ranar 25 Mayu 2018, (za a manta da dama).

    France Médias Monde sun samar da Akawun Kariyar Bayani, wanda shi ne kan gaba da za a tuntuɓa domin kariyar bayanin kai, a cikin Hukumar Kariyar Bayani ta Faransa (CNIL) da, a wani ɓangare, mutumin da abun ya shafa.

    Mutane na iya aiwatar da damarsu ta hanyar aika buƙata tare da shedar kamanni:

    • ta aikawa zuwa adireshin da ke tafe: France Médias Monde – Sashen Doka – Akawun Kariyar Bayani – 80 rue Camille Desmoulins – 92130 Issy les Moulineaux – Faransa (France)
    • ko ta hanyar imel zuwa: dpd@francemm.com

    Inda buƙatarka ta damar isa ga, gyara ko bamnbancin ra’ayi ke da alaƙa da bayanin da abokin ma’amalar France Médias Monde ya karɓa, muna kira da a tuntuɓi wannan abokin ma’amalar, a matsayin su na masu kula.

    Domin bayani a kan kariyar bayanin kai, ana iya tuntuɓar sashen yanar-gizon Hukumar Kariyar Bayani ta Faransa: CNIL.